19 Disamba 2025 - 15:56
Source: ABNA24
An Gudanar Da Mauludin Iyayen Annabi (S) Karo Na Biyu A Da'irar Katsina + Hotuna

A ranar Laraba 27/Jimada Thani/1447, daidai da 17/Disamba/2025, 'yan uwa na da'irar Katsina, suka gudanar da babban taron Mauludin Iyayen Annabi (S) karo na biyu wanda wasu gungun matasa (mawaƙa) na Fiyayyar Mata (Khadiman Iyayen Annabi (S) ke shiryawa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Taron ya gudana ne a Markaz ta Katsina, inda ya samu halartar manyan mutane daban-daban da suka haɗa da; Sheikh Sharif Al'alweey Kano (Mai Faɗimiya), Sheikh Kasim Abubakar Tsafe, Alhaji Sirajo, da sauran manyan baki daga ciki da wajen da'irar Katsina.

Sheikh Yakub Yahya Katsina ne, ya gabatar da jawabi bayan Sheikh Sharif Al'alweey Kano (Mai Faɗimiya) ya kammala na shi. Sheikh Yakub, ya fara da taya murna ga 'yan uwa, game da wannan babbar rana wadda aka ware ta, kuma aka assasa ta, domin gudanar da munasabar mauludin iyayen Annabi (S).

A jawabinsa ya bayyana cewa “Dalilin farko na assasa wannan taron shi ne, tunatar da al'ummar musulmi dangane da waɗannan bayin Allah da suka yi kyakkywan goyo, da kuma inganta tarbiyyar Matasa, shi ya sa aka kira abin, da ranar Iyaye ta duniya, sannan kuma sai bada kariya ga iyayen Manzon Allah (S). Ya ƙara da cewa, “Wasu sun kawo shawarar ace ‘Ranar Uwaye’ wasu kuma suka ce "Ranar Iyaye". Sai muka zaɓi ranar ‘Iyaye’ domin ‘Uwaye’ zai iya ta'allaƙa da mahaifa kawai, amma idan aka ce ‘Iyaye’ to zai haɗa har da dangin mahaifiya da mahaifi." Inji Sheikh Yakub.

Har wayau a jawabin nasa yana cewa "Kamar yadda Sharif ya yi mana bayani, a cikin iyayen Manzon Allah (S) babu guda ɗaya wanda ya zama baragurbi, ‘bal ma Ausiya'u ne’ kowannen su wasiyyi ne, Abdul-Muɗallib (AS) wanda shi ne kaka ga Manzon Allah (S) na kurkusa, kasantuwar sa wasiyyi, ya bar abubuwa da yawa waɗanda Alƙur'ani ya tabbatar da su. Alal misali: Yanke hannun Barawo. Shi ne ya fara ƙaddamar da wannan hukuncin, kuma Alƙur'ani ya kawo hakan."

“Sannan Abu-Ɗalib (AS) shi ma ya zo ya karɓi wannan aikin, a matsayin wasiyyi, daga cikin babbar wasiyyar da ya karɓa hadda rike Manzon Allah (S). Lokacin da zai yi wafati yana cewa: "Na bar maku ɗaukakar duniya, wadda zaku mulki duniya, da mutanen duniya a karkashin ta, shi ne wannan. Sai ya nuna Manzon Allah (S)."

Sheikh Yakub ya kara da cewa "Saboda haka mu a wajen mu, a I'itiƙadinmu, Iyayen Annabi ’yan aljanna ne, ‘bal-ma’ su ne za su raba aljannar. Mu wannan shi ne I'itiƙadinmu, kuma shi ne Imaninmu, a kan shi zamu rayu Insha Allah, kuma a kanshi zamu cika, kuma a kanshi za mu haɗu da Allah maɗaukakin sarki. Bansan wani zagin da za'a yi ma Manzon Allah (S) da ya wuce ace ga inda iyayen shi suke (Wa'iyazubilla) mummunan waje......" Ya ambata cikin damuwa.

Bayan kammala sauraren jawabin Sheikh Yakub Yahya, an bayar da kyaututtuka ga shari'an da suka zo na ɗaya, da na biyu, da na uku, a matakin gasar wake ga iyayen Annabi da aka gudanar, inda Sharif Al'alweey da Sheikh Yakub suka jagoranci basu kyaututtukan.

Haka zalika Sheikh Yakub ya jagoranci bayar da kyauta ga Sharif Al'alweey Kano, da kuma Alhaji Sirajo, da'irar Niamey da sauransu Inda daga karshe aka ba Sheikh Yakub, tashi kyautar, sannan aka bashi babbar kyautar Jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) da nufin ya hannanta gare shi.

AzzahraWeek2025

Da’irar Katsina Najeriya

18/12/2025

Your Comment

You are replying to: .
captcha